Kwace mulki ko gwamnati abu ne da ya fi kasancewa mafi sauki a kan tafyar da shi idan aka kwatanta da irin dimbin kalubalen da ke tattare da hakan.
Wannan martani ne da tsohon babban hafsan rundunar sojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya maida wa shugabannin mulkin sojin kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali.
Ya ce karfin soja zai iya taimakawa ne kawai wajen yaki da ‘yan ta’adda da kwato yankuna daga hannun su, amma ba wai tafiyar da mulki cikin inganci ba.
Don haka, a cewar sa, karfin soja kadai ba zai wadatar ba.
Kafar labarai ta DWAfrica ta ruwaito cewa tsohon janar din ya ce yaki da ta’addanci na bukatar nagartaccen shugabanci, adalci, ci gaba, bayanan sirri, da kuma karfafa hukumomin cikin gida.
Ya ce abin tambaya a nan shi ne, shin ko gwamnatocin Nijar, Mali da Burkina Faso sun fi gwamnatocin farar hular da suka yi wa juyin mulki samun nasarar ciyar da kasashen gaba.
Leave a comment