Home Labarun Ketare Afirka Ta Kudu Na Neman Dala Miliyan 18.5 Daga Najeriya, Ghana Da Sauransu
Labarun Ketare

Afirka Ta Kudu Na Neman Dala Miliyan 18.5 Daga Najeriya, Ghana Da Sauransu

Afirka Ta Kudu Na Neman Dala Miliyan 18.5 Daga Najeriya, Ghana Da Sauransu

Kasar Afirka ta Kudu na fuskantar turjiya daga kasashen Ghana da Najeriya bisa yunkurinta na neman a biyata kudaden da ta ce ta kashe kimanin dala miliyan 18.5 wajen hidimar maido da “yan kasashen waje, inda kasashen biyu suka ki amincewa da matsayin na Pretoria.

Afirka ta Kudu dai na neman wasu kasashen Afirka da dama su biyata kudaden da ta kashe wajen maido masu da ‘yan kasashensu da ta yi a lokacin rikicin kyamar baki da ya faru a kasar a ‘yan watannin baya.

Ghana dai ta ki amincewa da bukatar, a yayin da Najeriya kuma ta ce ita ba ta ma karbi wata bukata irin wannan ba a rubuce daga gwamnatin Afirka ta Kudun.

Kasar Ghana kuma ta kara da cewa ita da kan ta ce ta dauki nauyin hidima da jigilar kwaso ‘yan kasar ta daga Afirka ta Kudun.

Bambance-bambancen da aka samu dangane da martanin da aka samu tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya na nuna karara irin rikicin difulomasiyya da rudanin da bukatar biyan kudaden ta jawo.

Kasashen Malawi da Ethiopia ma na cikin kasashen da Afirka ta Kudu ta mika wa irin wannan bukata a cewar wasu rahotannin.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Musulmai ’Yan Asalin Somalia Mazauna Amurka Sun Yi Murnar Nasarar Ilhan Omar A Zaben Tsakkiyar Wa’adi

*Musulmai ’Yan Asalin Somalia Mazauna Amurka Sun Yi Murnar Nasarar Ilhan Omar...

Dan Shugaban Uganda Na Son Ya Gaji Mahaifinsa

Ɗan shugaban ƙasar Uganda na son ya gaji mahaifinsa, wanda ya shafe...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Soma Yunkurin Zaben Sabon Shugaba

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wato United Nations Security Council, ya...