Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi kiran da a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro tare da bunkasa walwala da tattalin arziki domin magance ta’addanci da sauran matsalolin da ke barazana ga yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Ya nemi da a rika yin amfani da kafafen yada labarai wajen dakile farfaganda domin kara kwarin gwiwa ga rundunonin tsaro tare da hana tasirin duk wani abin da zai iya karfafa ayyukan ta’addancin.
Radda ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis a Katsina a yayin da yake bude taron daraktocin tsaro na jihohin arewa maso yamma karo na biyu wanda hukumar tsaro ta DSS ta shirya.
Gwamnan, wanda mataimakin sa, Faruk Lawal, ya wakilta, ya ce matsalolin tsaron da yankin ke fama da su na bukatar kwakkwaran martanin hadin gwiwa daga gwamnati, hukumomin tsaro da kuma al’umma.
Radda ya bayyana cewa jihar Katsina ci gaba mai ma’ana ta fuskar tsaro ta hanyar hadaddun matakan yaki da sasanci, yana mai cewa a lokacin suka karbi mulki, kimanin kananan hukumomi 26 na jihar na fuskantar hare-hare babu kakkautawa.
Ya ce jihar ta yi kaura daga halin da take a da na kashe-kashe da garkuwa da mutane zuwa ingantuwar zaman lafiya sabo da kwakkwaran hadin gwiwa da hukumomin tsaro, a yayin da gwamnatin sa ta zuba makudan kudade wajen daukar matakan shawo kan matsalar daga tushe ta hanyar shigo da bangarorin al’umma da sasanci.
Taron, mai taken ‘Mu Hada Kai Wajen Yaki Da Ta’addanci’, ya hado shugabannin tsaro, sarakunan gargajiya, wakilan kananan hukumomi, jami’an leken asiri da sauran masu ruwa da tsaki.
Leave a comment