Wata mata da ‘ya’yanta biyu da suka hada da mai shekaru 5 da mai watanni 3 da haihuwa, sun rasa rayukansu bayan wani ginin da ba a kammala ba ya fada wa gidansu da ke Dan Mani a gundumar Rigasa, Kaduna.
Lamarin ya faru ne a hanyar Abuja, Kwanar Mai Danino da ke yankin Rigasa da misalin karfe 3:30 na daren Alhamis.
Mijin matar, Abubakar Haruna, ya ce shi ba ya gida a lokacin da hadarin ya afku, yana gidan gudar matarsa.
Ya ce babbar diyarsa ce ta tayar da shi daga barci ta hanyar buga kofar gidan da yake inda ta sanar da shi cewa gini ya fada wa mahaifiyarsu.
A cewarsa, ya fito a dimauce ya tafi gidan kuma a lokacin da ya isa wurin, makwabta sun riga sun fara kokarin ceto iyalin nasa daga baraguzan ginin.
Sai dai ya bayyana cewa wadanda abin ya rutsa da su sun riga sun mutu a lokacin aka zakulo su.
A cewarsa, babu dayansu da ke da wata alamar rauni a jikjnsa saboda fadawar ginin a kan su.
Haruna ya bayyana cewa sunan matar tasa Takiyatu, mai shekaru 35, sai ‘ya’yansu biyu masu suna Salisu da Muhammad.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, sai dai dole su karbi abin da ya farun a matsayin wata kaddara daga Allah, su yi wa wadanda suka rasun addu’ar neman gafarar ubangiji.
Shi ma, da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban al’ummar Titin Abuja din, Kwanar Mai Dabino a yankin Rigasa, Sani Ayuba, ya ce mazauna wurin sun yi matukar bakin ciki da afkuwar hadarin.
Leave a comment