Home Labarai ADC Ta Ce Ta Gudanar Da Zaben Fidda Gwani A Jihar Katsina Cikin Adalci
LabaraiSiyasa

ADC Ta Ce Ta Gudanar Da Zaben Fidda Gwani A Jihar Katsina Cikin Adalci

Wani jagoran ADC na kasa kuma shugaban jam’iyyar a jihar Katsina, Alhaji Lawal Batagarawa, ya ce jam’iyyar ta gudanar da zabubbukan fidda gwani cikin gaskiya da adalci, yana mai musanta zargin aikata magudi.

A cewar jaridar Daily Trust, Lawal Batagarawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta JBC Hausa, inda ya bayyana cewa da ma dole ne wasu masu neman takarar su nuna rashin gamsuwa da sakamakon zabubbukan na fidda gwani, kuma dole ne a kowane zabe a samu masu nasara da marasa nasara.

Ya ce a matsayinsu na ‘yan siyasa, ba zasu yi kasa a gwiwa ba a kokarinsu na ganin an samu daidato tare da rarrashin wadanda suka nuna rashin gamsuwa da sakamakon zabubbukan fidda gwanin.

Batagarawan ya dage kan cewa babu gaskiya ko kadan cikin zargin da ake na aikata magudi a zabubbukan.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Barr. Abba Mangal Ya Kaddamar Da Kwamitin Yakin Neman Zabensa

Dan takarar kujerar majalisar tarayya na Katsina ta tsakkiya a zaben 2027...