Home Labarai Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din
Labarai

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarorin din-din-din a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa ta ranar Talata mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ofishin shugaban ma’aikan jihar, Abubakar Yaro Bindawa, a madadin mai rikon kujerar shugaban ma’aikan jihar, Malam Mas’ud Mustapha Banye.

Sabbin Manyan Sakatarorin, wato Permanent Secretaries, sun hada da Suleiman Adamu Gachi, Karamar Hukumar Kankia, Muhammad Usman, Daura, sai Abdul’aziz Salisu, Malumfashi.

Shi dai Abdul’aziz Salisu Malumfashi kafin nadin sa a kan wannan matsayi daraktan shashen labaru da al’amuran yau da kullum ne na gidan talabijin na jihar Katsina wato KTTV.

Mai rikon kujerar shugaban ma’aikan jihar ya bayyana cewa nade-naden sun biyo bayan amannar da gwamnatin ke da ita ta cewa mutanen za su yi iyakar kokarinsu wajen kara inganta aikin gwamnati a jihar.

Malam Mas’ud Mustapha Banye ya taya wadanda aka nadan murna tare da yi masu fatan samun nasara da jagorancin Allah wajen sauke nauyin da aka dora masu.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...

NJC Ta Dakatar Da Alkalin Kotun Nasarawa Tsawon Shekara Daya Ba Tare da Albashi Ba

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa, NJC, ta dakatar da Mai...