Shugaban Kasa Mafi Tsufa Da Dadewa A Kan Mulki Ya Dawo Gida Bayan Dogon Zama A Kasashe Waje
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ya koma gida a ranar Alhamis bayan dogon zaman da ya yi na tsawon sama da watanni biyu a kasashen waje.
Tafiyar shugaban kasar mai shekaru 93 a duniya ta janyo damuwa dangane da lafiyarsa da kuma gibin shugabanci a kasar da ke tsakiyar Afirka.
Shugaba Paul Biya ya sauka a filin jiragen sama na babban birnin kasar, Yaounde, a cikin wani jirgi da ya taso daga birnin Geneva na kasar Switzerland, bayan kwashe sama da makonni 10 a waje.
Biya wanda ya fi kowane shugaban kasa tsufa da shekaru a duniya, wanda kuma yake bisa kujerar mulki tun a shekarar 1982, ya soma mulkinsa karo na takwas ne a cikin watan Nuwamba bayan lashe zaben da ke cike da rashin amincewar bangarori da dama a watan Oktoba.
Shugaban ya bar kasar ne a ranar 7 ga watan Yuni bisa abin da ofishinsa ya bayyana a matsayin wani dan gajeren zaman hutu a kasashen turai, amma kuma wannan ne zamansa mafi tsawo a kasashen waje a tsawon shekaru 44 da ya yi yana mulki.
Leave a comment