Home Uncategorized *NFF Ta Kafa Kwamitin Binciken Dalilan Rashin Nasarar Super Falcons*
Uncategorized

*NFF Ta Kafa Kwamitin Binciken Dalilan Rashin Nasarar Super Falcons*

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta kafa kwamitin binciken dalilan da suka haddasa ci bayan kwallon kafa a kasar, musamman ta fuskar wasannin kasa da kasa.

Hakan kuma na da nufin binciken dalilan rashin nasarar babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar, Super Falcons, da ta gaza shiga gasar cin kofin duniya ta mata ta shekarar 2027.

Matakin ya biyo bayan fitar da Najeriya a wasan dab da na kusa da na karshe, wato quarter final, a gasar cin kofin Afirka na mata da ke gudana a kasar Morocco, kafin kuma Afirka ta Kudu ta sake doketa a wani wasan neman shiga wata gasar ta kasa da kasa da ci 2-1.

Dokewar da aka yi wa Najeriyar na nufin Super Falcons din ba za ta samu shiga gasar cin kofin duniya ta mata wadda za a gudanar a kasar Brazil a 2027 ba.

Hakan ya sauya tarihin Super Falcons din na samun shiga kowace gasar cin kofin duniyar tun daga lokacin da aka soma ta a shekarar 1991.

A cewar hukumar ta NFF, kwamitin zai binciki musabbabin koma bayan da kungiyoyin kwallon kafan Najeriya ke samu tare da gano dalilan dushewar kwazon kasar a gasannin kasa da kasa a baya-bayan nan.

Hukumar ta ce kwamitin zai kuma bayar da shawarwari tare da fiddo matakan da suka kamata a dauka wajen hana sake faruwar irin wannan gazawar a gasannin nan gaba.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles