Home Labarai Kudaden Tallafa Wa Ilimi Da Ake Bai Wa Jihohi Da Abuja
LabaraiRohoto Na Musamman

Kudaden Tallafa Wa Ilimi Da Ake Bai Wa Jihohi Da Abuja

Shin ko kun san cewa Shugaban Ƙasa ya bai wa kowace jiha aƙalla Naira biliyan 2.7 domin gina sabbin azuzuwa, gyara tsofaffin makarantu, da kuma horas da malamai?

Kusan Naira miliyan 90 kenan ga kowace daga cikin kananan hukumomi 774 da ke Najeriya.

Wadannan kuɗade sun bambanta da daunin kuɗaɗen wata-wata da jihohi da ƙananan hukumomi ke samu daga gwamnatin tarayya.

Idan jiharku ba ta aiwatar da wani sabon aikin gina makarantu ko gyaran tsofaffin makarantu ba, ku sani cewa ya kamata ku riƙa tambayar gwamnan jiharku ya bayyana yadda aka kashe kuɗin.

Haka kuma, idan ƙaramar hukumarku ba ta gina sabbin makarantu ko gyara waɗanda suke akwai ba a cikin watannin da ke tafe, ya kamata shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana yadda aka yi amfani da kuɗin.

Gwamnatin Tarayya ta fitar da wadannan kuɗade ne daga tanadin kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin man fetur.

Ana sa ran ganin aƙalla sabbin azuzuwa 4,600 a faɗin Najeriya a cikin watanni masu zuwa.

Idan babu wani aikin gina makarantu ko gyaran makarantu a jiharku ko ƙaramar hukumarku, za ku iya kai ƙorafi ga hukumar ICPC ko EFCC, ku nemi a bayyana yadda aka kashe Naira biliyan 2.7 da aka ware domin ayyukan makarantu.

Ku kasance masu lura!

Allah ya ba Najeriya Nasarar fita daga cikin matsalolin da suka dabaibayeta, ciki har da na shugaban.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...