Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, wato ABU, ta soma daukar matakan tabbatar da sahihancin takardun karatun daya daga cikin farfesoshinta, Arc. Abdullahi Abubakar, wanda dogon jerin kwalayen karatun nasa ya ja hankalin al’ummar da ke ciki da wajen jami’ar.
Jami’ar ta ce tana sane da yadda ake ta yada labaran takardun farfesan a kafafen yada labarai na zamani, wato social media kuma za ta sanar da matsayinta ga al’umma bayan kammala binciken da ya kamata a kan lamarin.
Daraktan sashen yada labarai na jami’ar, Awwal Umar, wanda ya tabbatar da soma binciken, ya ce jami’ar za ta yi cikakken bayani a lokacin da ya dace bayan tabbatar gaskiya a kan lamarin.
Ya bayyana cewa jami’ar ba za ta yi garajen bayyana komai ba a yanzu, har sai an kammala dukkanin binciken da ya dace.
Matakin ya biyo bayan rahotannin da ke yawo
a kan kafafen yada labai daban-daban da ke bayyana irin jerin takardun karatun da farfesan ke da su, wadanda suka hada da digirorin digirgir, wato PhD, guda biyar da digiri na biyu, wato Masters, guda biyar, digirin farko guda bakwai, da takardun diploma 11 da dai sauran takardun karatu.
Dogon jerin takardun karatun ya jawo hankula da dama, musamman ganin matsayin farfesan a jami’ar da shigarsa cikin harkokin koyarwa da bincike da sauran ayyukan malanta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito dukkanin kokarin da aka yi na samun cikakken bayani daga farfesan ya ci tura domin dukkanin kiraye-kirayen da aka yi masa ta waya babu amsa.
Ko da yake, a martaninsa dangane da sakon text da aka tura masa na neman ya ce wani abu a kan batun, farfesan ya nuna cewa yana sane da bukatar amma ba zai iya cewa komai ba a halin yanzu.
Leave a comment