Home Labarai NJC Ta Dakatar Da Alkalin Kotun Nasarawa Tsawon Shekara Daya Ba Tare da Albashi Ba
Labarai

NJC Ta Dakatar Da Alkalin Kotun Nasarawa Tsawon Shekara Daya Ba Tare da Albashi Ba

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa, NJC, ta dakatar da Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir, alkali a Babbar Kotun Jihar Nasarawa, na tsawon shekara 1 ba tare da albashi ba.

Hakan ya biyo bayan samunta da laifin umartar kama tare da tsare wani mai shigar da kara na tsawon kwanaki 58 ba tare da bin matakan shari’a da doka ta tanada ba.

Haka kuma, NJC ta hana alkalin samun damar daga matsayinta zuwa wata babbar kotu na tsawon shekaru uku, bayan bincike ya tabbatar da cewa matakin da ta dauka ya saba wa ‘yancin wanda ake kara na samun adalci da damar kare kansa.

Lamarin dai ya faru
ne a cewar rahoton kwamitin binciken NJC, bayan alkalin ta bayar da umarnin kama wanda ake kara bisa zargin kin bin umarnin kotu, amma ba tare da fara shari’ar raina kotu yadda doka ta tanada ba.

Hukumar ta bayyana cewa ba a gabatar wa mutumin da takardun sanarwa na musamman da aka fi sani da Forms 48 da 49 ba, wadanda ake bukata kafin daukar matakin hukunta mutum kan raina kotu.

NJC ta kuma gano cewa zargin raina kotun ya faru ne a wajen zaman kotu, don haka bai halatta alkalin ta yi amfani da ikon hukunta shi kai tsaye ba tare da bin tsarin shari’a ba.

Baya ga Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir, NJC ta kuma dakatar da wasu alkalai biyu na tsawon shekara guda ba tare da albashi ba.

Alkalan sun hada da Grand Kadi Mohammed Sani Salihu na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa, bisa zargin wuce gona da iri wajen sake bude hukuncin da wata kotun Abuja ta riga ta yanke.

Sai Mai Shari’a Sobere Biambo na Babbar Kotun Jihar Rivers, bisa bayar da umarnin kama wasu masu kara da kuma cin tararsu Naira 300,000 kowannensu a rikicin farar hula wato Civil Case, ba tare da bin ka’idojin shari’ar raina kotu ba.

Haka kuma, an hana Mai Shari’a Biambo samun karin girma zuwa wata babbar kotu na tsawon shekaru uku.

A cewar jaridar Punch, matakin ya biyo bayan taron NJC karo na 112 da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamba, 2026, karkashin jagorancin Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...