Fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake Kaduna, Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya maganta a kan mabambantan ra’ayoyin jama’a cewa ko ya kamata malaman addinin musulunci su shiga a dama da su cikin siyasa ko kuma su tsaya kawai kan yin wa’azi ga al’umma.
Tattaunawa a kan wannan batu dai ta zafafa ne biyo bayan shigar wadansu malaman cikin harkokin siyasa, abinda ya ci gaba da jawo ra’ayoyi daban-daban a tsakanin musulmai, musamman a arewacin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin fitattun malaman da suka tsunduma cikin siyasa kuma suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar zabe akwai tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isah Ali Fantami da malamin nan dake Sakkwato, Sheikh Bashir Ahmad Sani, wadanda a cikin watan Fabrairun 2026 suka bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar gwamna a zaben 2027.
Akwai kuma sauran wasu sanannun malaman da suka rike ko suke rike da mukaman siyasa daban-daban a wasu jihohin.
Amma a cikin dukkaninsu, batun Fantami ya fi jan hankalin jama’a.
A yayin da masu sukar tunanin malamai na shiga siyasa ke da ra’ayin cewa fagen na da matukar muni da raba kawunan shugabannin addini, masu goyon bayan matakin sun dage kan cewa bai kamata malamai su rungume hannuwa ba a lokacin da kasar ke fama da matsalar rashin kyakkyawan shugabanci.
Masu sukar matakin dai na bayyana cewa siyasa na zubar da mutumcin malamai ta jifarsu da munanan malamai na siyasa, wanda a cewarsu, zai iya dushe kimarsu da girman da suke da shi a cikin al’umma.
A cewarsu, abin da kawai ya fi dacewa da malaman shi ne su zama masu samar da jagoranci da shawarwarin ilimi gami da sassaita shugabanni ta hanyar fadakar da su a kan hakkokin al’umma da suka rataya a wuyansu.
Masu goyon bayan shigar malamai siyasar kuma, sun dage kan cewa ba a iya samar da canji daga wajen gwamnati kadai, sai dai idan mutane masu sanin ya kamata sun shigo sun bayar da gudumawar da ta dace wajen canja alkiblar kasar.
Sun kara da cewa idan malamai na da ilimi, da mutumci da kwarewar da zasu iya shugabanci, ya kamata a basu damar neman mukaman siyasa ta hanyar shiga zabe domin su bayar da gudummuwa kai tsaye a maimakon kasancewa kawai masu gudanar da hudubobi da wa’azozi da addu’o’i.
Kasancewar tsohon minista Pantami a matsayin dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP ya kara jawo hankali da ra’ayoyi daban-daban a tsakanin al’umma a baya-bayan nan.
A sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a kan batun, Sheikh Gumi, wanda ya bayyana ra’ayin sa ta shafinsa na Facebook a ranar Litinin, ya dage cewa ba kuskure ba ne ko laifi malaman addini su shiga a fafata da su cikin harkokin siyasa.
A cewarsa, abu ne ma da ya fi dacewa, malamai su shiga siyasar a maimakon kawai su rika yi wa ‘yan siyasa addu’a daga waje.
Leave a comment