Home Labarai Majalisar Dinkin Duniya Ta Soma Yunkurin Zaben Sabon Shugaba
LabaraiLabarun Ketare

Majalisar Dinkin Duniya Ta Soma Yunkurin Zaben Sabon Shugaba

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wato United Nations Security Council, ya soma bin hanyoyin zaben sabon Sakatare Janar na majalisar dinkin duniyar.

Kwamitin ya soma ne da wani kwarya-kwaryar zabe domin auna karfin goyon bayan da ‘yan takarar kujerar su 7 ke da shi na darewa babbar kujerar.

Biyo bayan zagayen farko na kada kuri’ar, jakadun kasashe 15 dake cikin kwamitin sun yi gum da bakunansu dangane da sakamakon zaben wanda aka gudanar cikin sirri.

Mata 4 da maza 3 ne ya zuwa yanzu ke takara domin gadar Sakatare Janar mai ci, Antonio Guterres, wanda zai kammala wa’adin sa na biyu na shekaru 5 a ranar 31 ga watan Disamban 2026.

‘Yan takarar 7 sun hada da Michelle Bachelet ta kasar Chile, Maria Espinosa ta Ecuador, Rafael Grossi daga Argentina, Rebecca Grynspan ta kasar Costa Rica, Olara Otunnu daga Uganda, Carolyn Rodrigues-Birket ta Guyana da kuma Macky Sall na kasar Senegal.

Ko da yake Grossi, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, shi ne ke da sunan da ya fi yin fice, masu lura da al’amura sun yi imanin cewa a halin yanzu babu wani dan takarar da ake yi wa fifitawar da za ta iya kaiwa har lokacin da za samu canjin shugabanci a majalisar.

Shugaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar kuma jakadan kasar Congo Kinshasa, Zenon Ngay Mukongo, ya ce ba zai bayyana sakamakon zaben zagaye na biyu ba sai nan da wasu kwanaki masu zuwa.

Ya kara da cewa za a sanar da sakamakon zaben farko ne kawai ga kasashen dake zaben fidda ‘yan takarar, ba tare da fitar da shi ba ga jama’a.

Jakadun sun ki yin hasashen sakamakon zaben ne sabo da matsayin kasashe 5 mambobin din-din-din a kwamitin tsaron da suka hada Amurka, Rasha, China, Faransa da Birtaniya, da ba su riga suka nuna wanda suke so ba.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...