An yi kira ga gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda da ta tallafa wa masu sana’ar kayan nauyi ta la’akari da muhimmancin ta wajen kawar da shara da inganta rayuwar matasa da bunkasa tattalin arzikin al’umma.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin mai magana da yawun kamfanin harkar kayan nauyi na Jakutu Scraps Nigeria Limited dake Katsina, Muhammad Kanada, a sa’ilin wata ganawa da ‘yan jaridu a ranar Laraba.
Ya ce sana’ar kayan nauyi na taimakawa wajen dauke hankalin matasa daga aikata munanan laifukka da basu kwarin gwiwar neman na kansu da dogaro da kawunan su.
Kanada ya kara da cewa sana’ar kayan nauyin na bai wa daruruwan matasan jihar Katsina damar taimaka wa kawunan su da iyayen su, ciki har da daukar nauyin kudaden karatun su.
Ya kuma bayyana irin hanyoyin da suke bi wajen tabbatar da da’ar matasan da ke aiki tare da su, da suka hada da dakatarwa da sauran nau’o’in hukuci ga duk wanda aka samu da rashin gaskiya ko daukar kayan wani.
Ya ce suna hada gwiwa da jami’an tsaro wajen tabbatar da ganin sana’ar na gudana cikin tsafta kamar dai yadda gwamnati ta bayar da umarni.
Mai magana da yawun kamfanin Kayan Nauyin na Jakutu Scraps Nigeria Limited, ya yi kira ga wasu daga cikin masu irin wannan sana’a da Allah ya ba damar samun mukaman siyasa ko na gwamnati da su yi amfani da damar wajen tallafa wa ci gaban sana’ar ta hanyar jawo hankalin gwamnati ta wannan fuska domin amfanin al’umma baki daya.
Ya yaba wa ministan gidaje da tsara birane, Injiniya Muttaqah Rabe Darma, bisa ziiyarar da kawo masu kwanakin baya tare da yi masu alkawarin samun tallafin gwamnatin tarayya.
Ya ce a kullu yaumin matasa hamsin zuwa dari da wani abu na yin aiki a kamfanin su domin samun na kashewa da rage zaman banza.
Muhammad Kanada wanda ya bayyana cewa kungiyar ‘yan kayan nauyi na da dubban mambobi a fadin jihar, ya bayar da tabbacin goyon baya da hadin kan su ga shirye-shiryen gwamnati, musamman wadanda za su bunkasa sana’o’i da rayuwar matasan jihar.
Leave a comment