Home Uncategorized Mu Tattaru Mu Kawo Karshen Mulkin Danniya A Jihar Katsina – Alhaji Wada Mai Kaji Malumfashi
Uncategorized

Mu Tattaru Mu Kawo Karshen Mulkin Danniya A Jihar Katsina – Alhaji Wada Mai Kaji Malumfashi

Jam’iyyar PDP a Malumfashi ta yi kira da babbar murya ga matasa da sauran al’umma da su yi wa kansu kiyamullaili su zabi Sanata Yakubu Lado a matsayin gwamnan jihar Katsina a zaben 2027.

Wani babban jigon jam’iyyar a karamar hukumar, Alhaji Wada Mai Kaji, ne ya yi wannan kira a lokacin wani taron da ya shirya a ranar Lahadi a kofar gidansa dake garin Malumfashi.

Wada Mai Kaji wanda ya yi matukar godiya ga dandazon mutanen da suka halarci taron, ya gargadi matasa da sauran al’umma da su hankalta a zaben 2027 su zabi masu tausayinsu, ba wadanda za su ci gaba da azabtar da su ba.

Ya ce ya kamata mutanen jihar Katsina su farka daga barci, su kuma san abin da suke ciki ta hanyar kawar da mulkin zalunci na jam’iyyar APC a zaben mai.

Ya bayyana Sanata Yakubu Lado a matsayin wanda zai ceto su daga mummunan halin da mulkin APC ya jefa su a ciki.

Mai Kaji ya kara da cewa duba da irin gudummuwa da tallafi iri-iri da Sanata Yakubu Lado ke bai wa al’umma tun ma kafin yanzu kuma ba tare da yana rike da wata kujera ba, alamu ne na cewa idan ya samu dama zai yi abin da ya zarce hakan.

Ya ce Sanata Lado ya giggina hanyoyi a sassa daban-daban na jihar Katsina tare da biyan daruruwan miliyoyin nera na karatun dalibai marasa karfi dake manyan makarantu, inda a kwanannan ma ya yi odar fitulun sola sama guda dubu 13 da 600 domin rabawa ga kananan hukumomin jihar 34.

Da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Malumfashi, Alhaj Sama’ila Yarteba, ya yi kira ga al’umma da su bai wa Yakubu Lado damar zama gwamnan jihar Katsina domin shi kadai ne zai iya cire masu kitse daga wuta a daidai wannan lokaci da gwamnatin APC ta saka su cikin tsananin talauci, yunwa da rashin tasaro.

Shi ma dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar, Malam Lawal Assalamu Alaikum, a sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa, ya ce shi ko ba a zabe shi ba, a zabi Sanata Yakubu Lado da sauran ‘yan takarkarun da ke sama da shi, zai zamo mai ba su shawarwari na gari domin ya san za su dauka kuma za su yi aiki da su yadda ya kamata wajen share wa talakawa hawaye.

Ya ce hana mai zalunci ci gaba da zalunci ai ibada ce, don haka dakatar da mulkin APC a jihar tamkar jihadi ne da zai kawo sauki da zaman lafiya ga al’umma baki daya.

Taron ya samu halartar dimbin matasa da mata da dattawa da sauran magoya bayan jam’iyyar daga lungu da sakon karamar hukumar ta Malumfashi, inda duk sauran wadanda suka yi jawabai suka yi ittifakin cewa kawar da gwamnatin APC tare da maido da gwamnatin alheri ta PDP shi ne kadai mafita ga al’ummar jihar Katsina.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

*NFF Ta Kafa Kwamitin Binciken Dalilan Rashin Nasarar Super Falcons*

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta kafa kwamitin binciken...