Home Labarai An Dakatar Da Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya, NSCDC, Na Jihar Neja Daga Aiki
Labarai

An Dakatar Da Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya, NSCDC, Na Jihar Neja Daga Aiki

Ministan Harkokin Cikin Gida Na Najeriya, Olubunmi Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC na jihar Neja, Suberu Aniviye, daga aiki nan take.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wasu matasa su kimatin 37 da hukumar ta kama da zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba tare da kulle su a ofishinta da ke Minna, babban birnin jihara jihar.

Shi ma Gwamnan jihar, Umar Bago, ya kira wani taron ‘yan jaridu inda ya bayyana takaicinsa dangane da faruwar lamarin, yana mai bai wa jama’a hakuri da alkawarin gudanar da cikakken binciken musabbabin mutuwar da hukunta duk wanda ke da hannu wajen haddasa hakan.

 

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...