Home Labarai Hukumar Hana Fasa Kwauri Ta Najeriya Za Ta Maida Daukar Ma’aikata Shekara-Shekara – Bashir Adeniyi
LabaraiKasuwanci

Hukumar Hana Fasa Kwauri Ta Najeriya Za Ta Maida Daukar Ma’aikata Shekara-Shekara – Bashir Adeniyi

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya, Customs, ta ce za ta canza tsarin daukar sabbin ma’aikata zuwa na shekara-shekara a maimakon yadda take yi a da ba tare da amfani da wani kayyadadden lokaci ba.

Shugaban hukumar na kasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar da hakan a ranar Talata a lokacin wani taro da ‘yan jaridu a hedikwatar hukumar a Abuja jim kadan bayan fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasarar samun aiki da hukumar na shekarar 2024 zuwa 2025.

Ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na daidaita tsarin daukar ma’aikata da zai bai wa hukumar damar maye gurbin jami’an dake ritaya kan lokaci tare da bai wa sabbin jini damar shiga aikin hukumar a kowane lokaci.

A cewar Adeniyi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, hukumar ta yi wancakali da tsohon tsarin daukar ma’aikata wanda a karkashinsa ake daukar tsawon shekaru kafin masu sha’awar shiga aikin su samu damar yin hakan.

Ya bayyana cewa sabon tsarin zai maida aikin daukar ma’aikata a hukumar ya zamo na yau da kullum, a yayin da ake sa ran soma na shekarar 2026 na gaba kadan a cikin wannan shekara.

Leave a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Sabbin Manyan Sakatarorin Din-Din-Din

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin...

‘Yan Najeriya Sun Yi Wa Shugaban INEC Ihu A Birnin London Na Kasar Ingila

Wasu yan Najeriya da suka gudanar da zanga-zanga a birnin Landan sun...

Gaisuwar Ban Gajiya Da Godiya A Gareku – Bishir Kabir Murja

Ni Hon. Bishir Kabir Murja, a madadina da iyalaina da ‘yan uwana,...

Aikin Tsaron Cikin Gida Na ‘Yan Sanda Ne Ba Sojoji Ba – Janar Christopher Musa

Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa sojojin...