Ministan Harkokin Cikin Gida Na Najeriya, Olubunmi Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC na jihar Neja, Suberu Aniviye, daga aiki nan take.
Hakan ya biyo bayan mutuwar wasu matasa su kimatin 37 da hukumar ta kama da zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba tare da kulle su a ofishinta da ke Minna, babban birnin jihara jihar.
Shi ma Gwamnan jihar, Umar Bago, ya kira wani taron ‘yan jaridu inda ya bayyana takaicinsa dangane da faruwar lamarin, yana mai bai wa jama’a hakuri da alkawarin gudanar da cikakken binciken musabbabin mutuwar da hukunta duk wanda ke da hannu wajen haddasa hakan.
Leave a comment