Jam’iyyar ADC ta ce ta samu rahotanni a kan shirin da ake na kama Sakataren ta na Kasa, Ra’uf Aregbesola kafin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar a ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ta ce ya zamo dole su dauki rahoton da muhimmanci ganin yadda gwamnati ke yin gaban kanta wajen tafiyar da al’amurran jam’iyyun adawa ta hanyar taka dokar kasa.
Aregbesola dai tsohon gwamnan jihar Osun ne, tsohon minista, kuma sakataren jam’iyyar adawa ta ADC na kasa.
Don haka idan har wata hukumar tsaro tana da wani dalili na doka da take son gayyatarsa a kai, akwai shimfidaddun ka’idojin yin hakan.
Sanarwar ta kara da cewa kamun wanda ake kokarin yi a jajiberin zaben da jam’iyyarsa ke takara zai jawo zargin cewa manufar hakan ita ce hana shi jagoranci da kula da harkokin zaben jam’iyyar.
Kuma muna tabbatar wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro cewa idanun ‘yan Najeriya fa na kan zaben na Osun, sannan duk abin da ya faru tun daga farko har bayan zaben na ranar Asabar, za a danganta shi ne da abin da aka yi yanzu, ba wai bayanan da za a yi wa al’umma daga bisani ba.
Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin jam’iyyar APC dole ne ta kauce wa duk wani abin da ka iya jefa jihar Osun cikin mummunan rikici domin kuwa Najeriya har yanzu a karkashin dimokuradiyya take, kuma ya kamata gwamnati ta tuna da hakan kafin ranar Asabar.
Leave a comment