An samu gagarumin sauyi a siyasar Amurka bayan kammala zaɓen da aka gudanar a ranar Talata, inda ’yan takarar Musulmi suka samu nasarar lashe kujerun majalisa a wasu jihohin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin ’yan takarar sun samu damar shiga majalisa a karon farko, yayin da wasu da ke kan muƙamansu suka sake samun nasarar zaɓe domin ci gaba da wakiltar al’ummominsu.
A wani ɓangare kuma, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nuna cewa a shirye yake ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi, ciki har da damar kin amincewa da wasu dokokin da Majalisa za ta gabatar masa.
Wannan sakamako na ƙara nuna yadda wakilcin Musulmi ke samun ƙarin matsayi a fagen siyasar Amurka, musamman a matakin majalisa.
Leave a comment