Gwamnatin jihar Katsina ta fara aiwatar da ayyukan fasahar sadarwa ta ‘fibre optic’ ga al’umma a matsayin wani ɓangare na inganta harkar sadarwa a zamanance, tare da bai wa jama’a damar samun fasahar cikin sauki.
Sabuwar fasahar ‘fibre optic’ dai na nufin wani tsari ne na sadarwa da ake amfani da shi wajen samar da ingantaccen tsarin sadar da bayanai na zamani domin amfanin jama’a.
gwamnati jihar Katsina ta bayyana cewa yanzu harkar sadarwa ta zamani ta kasance wata sabuwar hanyar more rayuwa da ke jawo hannun jari da inganta kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire da samar da damamaki a fannonin tattalin arziki.
Da yake buɗe taron karawa juna sani na kwana ɗaya, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya yaba wa hukumar zuba jari ta jihar bisa shirya taron.
Mataimakin gwamnan wanda babban sakatare a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare, Alhaji Yusuf Ahmed, ya wakilta, ya yi ƙarin haske dangane da nasarorin da wannan gwamnati ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta samu wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari a jihar.
Ya kuma ƙara da cewa yanayi mai kyau da aka samar ga masu zuba jari ya taimaka matuƙa gaya wajen jawo hankalin masu zuba jari da kamfanoni ta hanyar ba su damar zuba hannun jari a jihar Katsina.
Tun da farko, da yake jawabi a wajen taron ƙarawa juna sanin na kwana ɗaya, shugaban hukumar zuba jari ta jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jikanshi, ya bayyana cewa wannan tsarin na ‘fibre optic’ abu ne da zai jawo hankalin masu zuba jari a jihar.
Kafar yada labarai ta Popular Hausa ta ruwaito cewa, taken taron shi ne “Samar da yanayi mai kyau don baje fasahar sadarwa ta ‘fibre optic” wanda ya ce zai samar da haɗin gwiwa da kamfanonin sadarwa na internet da masu lura da ayyukan su da kuma masu ruwa da tsaki akan harkokin sadarwa.
Alhaji Ibrahim Tukur Jikanshi ya ƙara da cewa dalilin shirya wannan taro shi ne domin a gano masu damar zuba hannun jari a wannan fasaha ta fibre optic’ wanda zai bunƙasa harkokin sadarwa a ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina
A cewar sa, taron zai bada haske da fahimtar da masu sha’awar zuba jari da abubuwan da ake buƙata domin faɗaɗa fasahar fibre optic’ tare da yin amfani da kasuwanci a wurare kamar manyan makarantu da gidaje da sauran su.
Leave a comment