Bayyana Gwamna Ademola Adeleke na Jam’iyyar Accord a hukumance da hukumar zabe ta kasa, INEC, ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun na ranar Asabar, rigimar wa zai karbi ragamar tafiyar da harkokin jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa ta zo karshe.
Daga farko dai kimanin jam’iyyu 15 ne suka shiga takarar amma sai a ranar zabe aka tabbatar da cewa yakin na ‘yan takarkari uku ne kawai daga jam’iyyu uku da suka hada da Accord, APC da ADC, wato Ademola Adeleke, Munirudeen Oyebamji da Najeem Salaam.
Babban Jami’in tattara sakamakon na hukumar INEC, Farfesa Joshua Ogunwole, a yayin sanar da sakamakon, ya ce Adeleke ya samu kuri’u dubu 511 da 067, a yayin da mai bin sa, Bola Oyebamji na APC, ya samu kuri’u dubu 444 da 815, sai kuma Najeem Salaam na ADC ya zo na uku da kuri’u dubu 17 da 180.
Da yake maida martani kan nasarar da ya samu, Adeleke ya yi rokon maido da cikakken zaman lumana da hadin kai tsakanin al’ummar jihar Osun domin maganin raunin rikicin da yai ta faruwa kafin zaben, a yayin da ya yi alkawarin fadada ci gaban jihar da samar da karin romon dimokuradiyya a karkashin mulkinsa.
A sa’ilin da yake jawabi ga ‘yan jaridu bayan samun nasarar, gwamnan ya yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa tsayawa kan tabbatar da zaben gaskiya da adalci.
Rahotanni sun yi nuni da cewa gwagwarmayar da aka yi wajen sake zaben Adeleke ba abu ne da ya kasance mai sauki ba.
Daga rikicin jam’iyyar sa ta da, PDP, wanda ya yi tsanani da sanadiyyar sauya shekarsa zuwa jam’iyyar Accord, zuwa shari’o’in da suka dabaibaye cancantar Accord din ta sanya dan takara, a karshe dai Adelake ya samu tsallake dukkanin wadannan shingaye tare da cika sharuddan hukumar INEC na shiga jerin ‘yan takara a zaben.
Hakanan kuma, matakin kafin zaben ya sha fama da rikicin siyasa inda har wasu suka rasa rayukan su, da dama kuma suka samu raunuka, a yayin da jam’iyyun Accord da APC ke fama zarge-zargen juna a kan kai hare-haren magoya baya a lokacin yakin neman zaben.
A sabili da irin halin rikicin da jihar ta shiga a lokacin, an yi ta tura dimbin jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron rayukan al’umma da jami’an hukumar zabe, INEC, da kuma masu sa ido a kan zaben
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa duk da ‘yan matsalolin da aka samu da na’urorin BVAS a lokacin zaben, sakamakon da aka saki ya nuna karin karbuwar Adeleke bisa zaben farko na shekarar 2022, inda ya samu kuri’u kimanin dubu 403 da 371 tare da doke gwamnan APC mai ci a lokacin kuma yanzu ministan tattalin arzikin teku, Alhaji Isiaka Oyetola.
Sai ga shi a zaben wannan shekara ta 2026, kuri’un da Adeleken ya samu sun zarce dubu 511, sannan tazararsa a wannan karo tsakanin sa da mai bin sa, ta lunka ta shekarar 2022.
Daga cikin kananan hukumomin jihar 30, Adeleke ya lashe guda 19, wanda ya zarce guda 17 da ya lashe a wancan zaben na 2022.
Ana ganin Adeleke ya samu wannan gaggarumar nasara ne, a cewar masharhanta, sabo da inganta jin dadin ma’aikata ta hanyar biyan su albashi da fansho a kan kari gami da aiwatar da dimbin ayyukan raya kasa fadin jihar.
Leave a comment