Ɗan shugaban ƙasar Uganda na son ya gaji mahaifinsa, wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkin ƙasar
Shugaban rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen shekarar 2031, shekaru biyar kafin lokacin zaɓen.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Muhoozi mai shekaru 52 ya bayyana hakan ne cikin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce yana da yakinin zai lashe zaɓen.
Matakin ya sake jawo hankali kan batun makomar shugabancin Uganda, musamman kasancewar mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkin ƙasar.
Leave a comment